Guguwar Haiyan wadda ta yi ɓarna a Philippine ta afka wa Vietnam | Siyasa | DW | 11.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Guguwar Haiyan wadda ta yi ɓarna a Philippine ta afka wa Vietnam

Mahukuntan Phillippine sun fara ƙoƙarin kawo sauƙi ga waɗanda mahaukaciyar guguwar Haiyan ta afka musu a ƙasar duk da cewa suna fiskantar ƙalubale na kai tallafi ga waɗanda abin ya fi shafa

Bayan da mahaukaciyar guguwar da akewa laƙabi da Haiyan ta afka ƙasar Phillipine, an wayi gari ana cigaba da kwashe gawawwakin waɗanda guguwar ta rutsa da su, a yayinda waɗanda suka rasa matsugunnensu kuma suke fafutukar neman abinci, da ruwan sha da magunguna. Sai dai duk da cewa 'yan sanda da masu aikin agaji na ƙoƙarin daidaita lamura, har yanzu akwai ƙorafin samun jinkiri wajen raba kayayyakin tallafi ga waɗanda ke buƙata.

A lardin Leyte dake cikin garin Tacloban inda mahaukaciyar guguwar ta fi ta'adi, ana kyautata zaton aƙalla mutane dubu 10 ne ke neman tallafi cikin gaggawa. A jimilce mutane aƙalla dubu 400 ne basu da wuraren kwana ko ma na sawa bakin salati, mutane milliyan huɗu ne suka yi gwagwarmayar ceto rayuwarsu bayan da guguwar ta afka ƙasar ta Phillipin, waɗanda a yanzu haka kuma zasu sake shiga wata sabuwar gwagwarmayar ta rayuwa saboda irin sabon ƙalubalen da za su fiskanta

Ana aikin kaye-kaye a lardin Samar inda ake kwashe kayyaki irin su katako, da wayoyin wutar lantarki, kuma bisa yadda abubuwa ke tafiya kamar ba za a taɓa kammala wannan aikin ba. Layoyin wuta sun katse, babu tsabtataccen ruwan sha, kana kuma babu hanyoyin sadarwa na waya. Ko da shi ke ana cikin wanann yanayi a Samar, sai aka sami labari mai daɗi a tacloban wanda ke cewa za a tayar da ɗaya daga cikin tashoshin sadarwar dake Tacloban yadda mutane zasu iya samun labarin 'yan uwa da abokan arziƙi amma duk da haka, akwai sauran aiki a gaba tunda ko ɗaya basu da abinci, ɗungun basu da ta yi a cewar wannan mutumin wanda guguwar ta rutsa da shi

" Komai ya lalace, komai ya tafi, ni da 'ya'ya na ko rigunan sanyawa bamu da su"

Matakan da ƙasar ta ɗauka a halin yanzu

Shugaban ƙasar Phillipine Benigno Aquiono bai ɓata lokaci wajen zuwa inda guguwar ta fi yin ta'adi ba, kuma yayi alƙawarin cewa zasu yi iya ƙoƙarin wajen taya mutane kwasar dukiyoyinsu da suka ragu. Wannan kuwa zai yi wahala, saboda yawancin 'yan sandan dake Tacloban basu zo aiki ba amma kuma Aquino ya ce za a tallafawa duk waɗanda guguwar ta rutsa da su.

" Abin takaici ne cewa ba a ga mutane da yawa ba, kuma wasu da dama sun hallaka, kamar yadda alƙaluma suka nuna, amma kuma dole ne mu fara da biyan bukatun waɗanda suka rayu, musamman waɗanda suka yi rauni da waɗanda suke buƙatar abinci da ruwan sha cikin gaggawa"

A Tacloban an tabbatar da mutuwar 300 a hukumance, waɗanda dole ne a kwashe su kada su janyo matsaloli, haka nan kuma da yawa daga cikin waɗanda suka rayun basu da ƙarfin taimakwa kansu kamar wannan matar

"Dole sai na sami taimako, bani da gida, bani da kudi babu sauran wani abin da na mallaka"

Guguwar Haiyan ta koma ƙasar Vietnam

Duk da haka dai akwai sauran yankunan da ke bada tallafi, hukumomin ceto na ƙoƙarin kai ga waɗanda ke buƙatar tallafin gaggawa. Akwai kuma ƙungiyoyin agaji daga Manilla babban birnin ƙasar da kuma wasu ƙasashen waje waɗanda ke ƙoƙarin rabam tsabtataccen ruwan sha, magunguna bargon rufa da kuma tantuna sai dai babban ƙalubalen dake gabansu shi ne hanyoyin sufuri domin babu tsahar jirgin sama kuma duk tituna sun lalace.

Guguwar haiyan wadda ta yi ta'adi a yankunan da suka kai faɗin kilometa 600 ta ratsa zuwa ƙasar Vietnam. Guguwar ta yanka ne daga kudancin tekuncikin dare tana kaɗawa a gudun kilometa 120 cikin kowace sa'a zuwa gaɓan tekun ruwan. Hanoi na san ran ruwan zai yi ta'adi, amma kuma wata ƙila, ba zai kai irin wanda ya afku a ƙasar phillipine ba.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin