Guguwa ta jijjige bishiyoyi a Amirka | Labarai | DW | 01.04.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guguwa ta jijjige bishiyoyi a Amirka

Guguwar ta dirar wa garin Arkansa har sau biyu a ranar Juma'a, inda ta jijjige wasu bishiyoyi, ta kuma yi awon gaba da rufin wasu gine-gine sannan ta lalata motoci tare kuma da katse lantarki ga mutane wajen 90,000.

Hukumomin Amirka sun ce kimanin mutum 350,000 wata mahaukaciyar guguwa ta jefa cikin tararrabi a garin Little Rock, shelkwatar jihar Arkansa da ke kudancin kasar. Kawo safiyar Asabar din nan jaridar New York Times ta ruwaito cewa mutane uku guguwar ta yi ajalinsu, a yayin da mutum 30 suka ji munanan raunuka.

Gwamnan jihar ta Arkansa Sarah Huckabee Sanders ta ayyana dokar ta baci, inda ta ce guguwar ta yi wa jama'a barna sosai, tana mai kira ga Amirkawa da ke zaune a yankin da su sanya ido sosai kan gargadin aukuwar guguwa da hukumomi ke fitarwa.