1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Guguwa ta yi ta'adi a tsibirin Solomon

Suleiman Babayo AH
April 5, 2020

An samo mutane biyar da suka mutu ana ci gaba da neman saura 27 sakamakon iska mai karfi a tsibirin Solomon da ya kife da jirgin ruwan fasinja sakamakon iska mai karfi a tsibirin Solomon.

https://p.dw.com/p/3aTUN
Global Ideas Solomon-Inseln Karettschildkröte
Hoto: DW/H. Goll

An samo mutane biyar da suka mutu yayin da ake ci gaba da neman saura 27 sakamakon iska mai karfi a tsibirin Solomon da ya kife da wani jirgin ruwan fasinja. Guguwar mai karfi tana ci gaba da yin barazana ga wannan karamar kasa ta tsibirin Solomon da ke kudancin tekun Pacific.

Tun ranar Jumma'a da ta gabata guguwa mai karfi ta kife da jirgin ruwan fasinja da ke dauke da mutane 738 kamar yada 'yan sandan tsibirin na Solomon suka tabbatar. Kuma ana sa ran kara samun irin wannan guguwa mai ta'adi wadda za ta sake wucewa ta wannan tsibiri.