Guguwa na yin barazana ga zaɓen Amirka | Labarai | DW | 27.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guguwa na yin barazana ga zaɓen Amirka

Hukumomi a Amirka na ƙoƙarin ɗaukar matakan yin kariya gabannin zuwan guguwar Sandy.

Mahaukaciyar guguwa nan da ke haɗe da ruwan sama da iska mai ƙarfin gaske, wacce ta ratsa yankin Karibiyan ta kashe mutane a ƙalla guda 40 a Bahamas da Jamaica da Haiti da Cuba da kuma jamhuriyar Dominikan.

Masu yin hasashe kan yanayi sun yi gargaɗin cewar a ƙarshen mako guguwar za ta iya yin tsananin muni a yankunan arewa maso gabashin Amirka inda ake zaton cewar za a samu zubar dusar ƙankara , abinda ake ganin zai iya zama cikas ga masu kaɗa ƙuria'a kafin lokaci zaɓɓukan shugaban ƙasar da za a gudanar. Kana kuma an ce guguwar zata faɗaɗa zuwa New York a ranakun Litinin da Talata mai zuwa.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal