Gudumawar APC ga inganta dimokradiyyar Najeriya
August 12, 2013Talla
Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya nuna alamun tsayawa takara a zaben 2015 idan gamayyar jam'iyyun adawa ta APC ta bukace shi da yin haka. Cikin wata hira da ya yi da wakiliyarmu ta Jigawa Zainab Shuaibu Rabo Ringim, janar Buahri ya yi alkawarin kyautata halin rayuwar 'yan Najeriya idan hakarsa ta cimma ruwa a zabe na gaba.
Janar Buhari, ya kuma bayyana cewar, za su dauki dukkan matakan da suka wajaba domin hana sojan gona karbe akalar tafiyar da harkokin jam'iyyar, tunda kuwa a cewarsa, sun koyi darussa da dama daga zabukan da suka gabata.
Mawallafiya : Zainab Shuaibu Rabo
Edita : Saleh Umar Saleh