Goyon bayan Jamus ga matakan Faransa a Mali
January 14, 2013Gwamnatin Jamus tana goyon baya da taimakon matakan soja da Faransa take dauka kan yan tawaye musulmi a kasar Mali, kuma tace tana nazari a game da yiwuwar baiwa Faransa din karin gudummuwar kayan yaki. To amma a wani bayani da gwamnati ta gabatar a Berlin, tace Jamus ba zata tura sojoji su shiga yakin dake gudana a kasar ta Mali ba.
Ba kamar a lokacin da rundunar kasa da kasa da tayi yaki a Libya a watan Maris na shekara ta 2011 ba, inda Jamus ta zama saniyar ware, a wannan karo gwamnati a Berlin ta fito fili ta baiyana cikakken goyon bayanta ga matakan soja da Faransa take dauka a Mali. Gwamnatin tace Faransa tana daukar matakai da suka dace kuma suka kamata a dauke su, wadanda burinsu shine a dakatar da kusantar da mayakan yan tawayen Mali suke yi ga babban birnin kasar Bamako. Ministan tsaron Jamus, Thomas de Maiziere yace tun da farko sai da Faransa ta sanarwa Jamus shirin ta, kuma Faransa din tana da cikakken goyon baya daga garemu. Shima ministan harkokin waje, Guido Westerwelle yace Turawa suna da matukar sha'awar ganin kasar ta Mali bata zama maboya kuma dandalin aiyukan yan tarzoma a yankin da ga baki ga hanci yake tsakanin sa da Turai ba. Gwamnati a Paris, inji bayani na Jamus, tana tafiyar da aiyukanta ne bisa dacewa da bukatun kudirin kwamitin sulhu na majalisar dinkion duniya. Ana kuma tattaunawa da Faransa game da fannonin da Jamus zata iya baiwa kasar taimako. kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin waje, Andreas Peschke ya nunar:
Yace irin wannan taimako alal misali, yana iya kasancewa ta hanyar baiwa Faransa kayaiyaki ne da take bukata a matakan na soja a Mali, ko taimakonta a fannin aiyukan likitoci da magunguna ko taimakon jin-kai. Wadannan sune abubuwan da musmaan aka cimma daidaitawa kansu.
To sai dai Jamus tace ba zata tura sojojinta su shiga yakin na Mali ba. Wannan kuwa mataki ne dake samun goyon baya har ma daga yan adawa a kasar ta Jamus, inda Jamus din tace wannan ra'ayi nata ya dace gaba daya da ra'ayin kungiyar hadin kan Turai. Kakakin gwamnatin taraiya, Steffen Seibert dake bayanin wannan matsayi na Jamus yace:
Sakamakon hadin kai na al'ada da dangantaka da kuma tarihin dake tsakanin Faransa da wannan yanki na nahiyar Afrika, uma musmman ganin cewar Faransa yanzu haka tana da rundunonin sojan ta da ta tsugunar dasu a wasu kasashe makwabtan Mali, Faransa din tana da huldodi na musamman, kuma tana da isassun sojoji a kusa da zasu iya tafiyar da wannan aiki.
Kakakin na gwmanatin yace wannan ma shi ya sanya Mali ta gabatar da rokon nata na tgaimako ne zuwa ga Faransa amma ba zuwa ga Jamus ba. Gwamnati a Berlin inji ministan tsaro Thomas de Maiziere, tana ma da ra'ayin cewar kamata yayi a gagauta baiwa matakan kawar da yan tawayen da suka mamaye arewacin Mali wata fuska ta yan Afirka. Saboda haka ne Jamus zata taimakawa kokarin soja da na siyasa da kungiyar ECOWAS ta kasashen Afirka ta yamma take yi kan rikicin na Mali. Yanzu haka dai ana ci gaba da rade-radi a game da irin taimakon da kungiyar ta ECOWAS zata nema daga Jamus, saboda ranar Laraba ake sa ran isar shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara a Berlin domin ziyarar da tuni aka shirya yinta. Ouattara shine shugaban ECOWAS a yanzu, kuma ana zaton zai yi amfani da tattaunawarsa da shugaban gwamnati, Angela Merkel domin gabatarwa Jamus rokon kungiyar. Jamus dai tuni ta baiyana shirin ta bada gudummuwa a rundunar da zata kunshi mutane 200 da za'a tura domin horad da sojojin Mali, bisa manufar karfafa zaman lafiya a kasar.
Mawallafi: Bernd Gräßler/Umaru Aliyu
Edita: Usman Shehu Usman