Gobarar daji na barna a Indunusiya | Labarai | DW | 19.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobarar daji na barna a Indunusiya

A kasar Indunusiya wata gobarar daji da ta taso tun makonni na neman gagarar kundila duk da agajin da kasashen duniya suka kawo wajen neman dakileta.

Gurbataccen hayakin gobarar ya soma yin illa ga kasashen Kudu maso Gabashin nahiyar Asiya irin su Singapor da Malesiya inda ta kai kasashen ga rufe makarantun boko da dama .

A makon da ya gabata ne dai a bisa matsin lambar kasashen duniya kasar Indunusiya ta amince da karbar dauki daga wasu kasashen makwabta domin kashe gobarar wacce rahotanni daga kasar ke cewa da gangan manoma ke tayar da ita a cikin fadamun kasar da nufin samar da filayen noma.

Sai dai ministan muhalli na kasar ta Indunusiya ya ce ko a nan gaba za a dauki akalla wata daya kafin murkushe wutar matsawar ba a samu ruwan sama ba.