Girgizar kasar mai karfi ta afka wa Kudancin Chile
September 17, 2015Girgizar kasa mai karfin maki 8.3 a ma'aunin Richter da ta afkawa gabar teku a Chile a daren jiya Laraba ta yi sanadin halaka mutane biyar da tilasta kimanin miliyan daya kauracewa muhallansu.
Wannan girgiza dai ta sanya jijjigar gine-gine a birnin Santiago da tazarar kilomita 280 daga Kudanci sannan wasu yankunan da ke a kusa da gabar teku sun shiga fargaba ta yiwuwar samun Tsunami.
Tuni dai shugaba Michelle Bachelet ta bayyana shirinta na ziyartar wurin da lamarin ya afku , wanda ke zama mafi muni a wannan kasa tun bayan wanda ta gani a shekarar 2010.
Masana dai sun bayyana cewa a zauna cikin shiri a yankunan da ke a Amirka ta Kudu da Hawaii da California duk da cewa torokon ruwa da ake tsammani zai dan lafa. An dai ga mutane a kasar ta Chile a kan tituna cikin rudani da firgici.