Girgizar kasa ta afku a Afirka ta Kudu
August 5, 2014Wata girgizar kasa da karfinta ta kai maki biyar da digo 3 a ma'aunin Richter ta afku a birnin Orkney na kasar Afirka ta Kudu inda ta kashe mutun guda. Jami'an agaji sun bayyana cewar wani gini da ya rifta ne ummal aba'isan mutuwar ita matar a wannan bala'i daga indallahi a yankin Arewa maso yammacin wannan kasa.
Sannan kuma kakakin Kungiyar agaji ta ER24 Luyanda Majija ta bayyana wa manaima labarai cewar dimbin masu hako ma'aidinai sun makale a ramukan hako arzikin na karkashin kasa, ba tare da yin wani karin haske ba.
Wannan girgizar kasar da ta afku a daidai karfe 11 da rabi agogon Najeriya da Nijar ta girgiza manyan gine-gine da dama a Johannesburg cibiyar cinikayyar Afirka ta Kudu. Sannan kuma a ji ruguginta a kasashen Mozambik da kuma Botswana.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman