Girgizar kasa ta afka wa Indunusiya | Labarai | DW | 02.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girgizar kasa ta afka wa Indunusiya

Zurfin girgizar dai da ta faru a kusa da gabar teku a tsibirin Sumatra ya kai mita 24, a cewar manazarta a harkar da ta shafi girgizar kasa a Amirka

Wata girgizar kasa mai karfin maki bakwai da digo tara ta afka wa kasar Indunusiya kamar yadda sashin da ke lura da harkokin da suka shafi girgizar kasa na Amirka ya bayyana a ranar Laraban nan.
Zurfin girgizar dai da ta faru a kusa da gabar teku a tsibirin Sumatra ya kai mita 24.
Idan dai ba a manta ba a shekarar 2004 kasar ta Indunusiya ta fiskanci bala'i na ambaliyar Tsunami, abin da ya yi sanadi na rayuka da dukiyoyin al'umma.

Heronimus Guru na kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce akwai wadanda suka rasu sai dai har yanzu ba a kai ga tantance yawan mutanen ba.