Girgizar kasa mai karfi ta afku a Indunisiya | Labarai | DW | 09.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girgizar kasa mai karfi ta afku a Indunisiya

Wannan bala'in ya Saba afkuwa a Indunusiya. Amma kuma a wannan karon babu fargabar igiyar ruwan Tsunami bayan girgirzar kasa a mashigin ruwan Banda.

Wata girgizar kasa da ta kai karfin maki bakwai a ma'aunin Richter ta afku a mashigin ruwan Banda Aceh da ke kasar Indonusiya. Ba a dai bayyana yawan mutane da suka rasa rayukansu ko kuma dukiya da ta lalace ba i zuwa yanzu. Sai dai kuma hukumomin Indunusiya sun bayyana cewar babu fargabar afkuwar ingiyar ruwan Tsunami

Ita dai Indunusiya ta saba fuskantar bala'in girgizar kasa mai karfin gaske, inda a shekara ta 2004 mutane dubu 170 suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa hade da igiyar ruwan Tsunami.