Gidauniyar taimakawa ƙasar Mali
February 5, 2013Yau ne wakilai daga ƙasashe 45, tare da ƙungiyoyn bada agaji na ƙasa da ƙasa ke shirya zaman taro a birnin Brussels na ƙasar Beljiyam domin tunanin hanyoyin taimakawa ƙasar Mali.Majalisar Dinkin Duniya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar gamayyar Afrika da ECOWAS su ka shirya wannan taro da zumar musanyar ra'ayoyin wanda za su fidda Mali daga halin da ta tsincin kanta, hasali ma, maida ƙasar bisa inganttatar turbar demokraɗiya, da kuma taimakawa dubunan 'yan gudun hijira da suka ƙauracerwa gidajensu.
A yanzu haka dai sojojin Mali tare da taimakon Faransa na cigaba da samun nasarori akan ƙungiyoyi da suka mamaye arewacin Mali.A nata ɓangare ƙungiyar Tarayya Turai ta yi alƙawarin aika tawagar ƙurrarun sojoji, domin horar ga dakarun Mali.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman