Ghani ya zama shugaban Afghanistan | Siyasa | DW | 22.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ghani ya zama shugaban Afghanistan

Bayan watanni ana zaman tararradi a kan sakamakon zaben shugaban kasar Afghanistan, daga karshe an bayyana cewa Ashraf Ghani ne zai zama sabon shugaban kasa.

Babban abokin hamayyarsa Abdullah Abdullah ne dai zai zamo sabon shugaban gwamnati. Matsin lamba daga kasar Amirka dai ya taimaka wajen kulla yarjejeniya tsakanin jiga-jigan 'yan siyasar biyu wadanda suka fafata yayin zaben shugaban kasar ta Afghanistan da aka gudanar a watannin da suka gabata.

Wannan yarjejeniyar ta tabbatar da Ashraf Ghani mai kimanin shekaru 65 a duniya kuma tsohon ministan kudi a matsayin sabon shugaban kasar wanda zai gaji Shugaba Hamid Karzai mai barin gado, yayin da Abdullah Abdullah tsohon ministan harkokin waje mai kimanin shekaru 54 a duniya zai kasance sabon shugaban gwamnati, wato mukamin firaminista da aka kirkiro bisa yarjejeyar ta raba madafun iko.

Jim kadan bayan yarjejeniyar shugaban hukumar zaben kasar Ahmad Yousuf Nouristani ya tabbatar da sabon shugaban kasar inda ya ce hukumar zabe mai zaman kanta ta tabbatar da Dr Mohammad Ashraf Ghani Ahmadzai a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar Musulunci Afghanistan.

An tseratar da kasar daga yaki

Shiga tsakanin da Amirka ta yi wajen kulla yarjejeniyar ya kawar da yuwuwar sake komawar kasar yakin basasa irin wanda aka fuskanta kafin shekara ta 2001, lokacin da Amirka ta jagoranci kutsen da ya kawar da gwamnatin Taliban bayan harin da aka kai da jiragen sama kan kasar ta Amirka wanda ake zargin kungiyar al-Qaeda da kaiwa. Samun gwamnati mai karbuwa a birnin Kabul abu ne mai mahimmanci, musamman yayin da ake shirin janye dakarun kasashen duniya daga karshen wannan shekara ta 2014.

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya nemi sabuwar gwamnatin ta Afghanistan ta saka hannu kan yarjejeniyar da za ta bai wa dakarun kasashen ketare damar horar da dakarun kasar ta Afghanistan. Duk da bayyana Ashraf Ghani a matsayin wanda ya lashe zaben, babu wasu alkaluma da ke nuna yawan kuri'un da kowanne dan takara ya samu.

Martanin al'ummar Afghanistan

Tuni 'yan kasar ta Afghnistan suka fara mai da martani inda suke da mabanbantan ra'ayoyi a kan raba madafun ikon tsakanin jiga-jigan 'yan siyasar:

"Na ji dadi matuka da wannan labari, duk 'yan Afghanistan suna murna da wannan yarjejeniya." "Ba mu ji dadi ba, wannan zabe ya kawo mana matsaloli daban-daban a kasarmu."

Ita kuwa kungiyar tsagerun Taliban masu gwagwarmaya da makamai watsi ta yi da yarjejeniyar kafa sabuwar gwamnatin. Lamarin da ke nuni da cewa 'yan kungiyar ka iya yin amfani da duk wani sabani da aka samu a gwamnatin hadakar wajen wargaza lamura a cikin kasar.