1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Asusun IMF ya ba da rance ga Ghana

Suleiman Babayo USU
December 13, 2022

Ghana da Asusun ba da lamuni na duniya IMF sun cimma matsaya na bai wa rance domin ta farfado da tattalin arziki wanda yake cikin matsaloli mafi muni a fiye da shekaru 20 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4KrvS
Ghana | Birnin Accra
Birnin Accra na GhanaHoto: Seth/Xinhua/picture alliance

A wannan Talata kasar Ghana ta cimma matsaya da asusun ba da lamuni na duniya kan karbar rancen kudi na kimanin dalar Amirka milyan dubu-3, domin farfado da tattalin arzikin kasar da yake masassara. Kasar da ke ynakin yammacin Afirka ta fuskanci tashin farashin kayayyaki na kimanin kashi 40 cikin 100 yayin da kudin kasar ya karye, abin da ke zama matsalolin tattalin arzikin mafi muni cikin kimanin shekaru 20 da suka gabata.

Matsalolin tattalin arziki suka tilasta gwamnatin Shugaba Nana Akufo-Addo sauya matsayi na rashin cin bashi daga kasashen ketere, inda gwamnati ta fita neman taimakon. Kana gwamnatin kasar ta Ghana ta yi karin harajin kayan da ake sayarwa a kasar.