Ghana: Shirin fara amfani da jirage marasa matuka | Zamantakewa | DW | 11.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ghana: Shirin fara amfani da jirage marasa matuka

A Ghana batun sabon tsarin amfani da Jirgi mai saukar ungulu maras matuki na cin karo da tirjiya a zauren majalisar dokokin kasar bayan da suka umarci ministan lafiyar kasar ya koma ya sake shiri kan batun.


Gwmnatin kasar Ghana dai ta kuduri aniyar amfani da Jirage masu saukar ungulu marasa matuka don harkokin kiwon lafiya a kasar ta hanyar rarraba magunguna da sauran bukatu na lafiya, shirin da aka yi kiyasin zai lakume kudi sama da Dalar Amurka Miliyan 20 a tsawon shekaru 5. Ba wai a majalisar ne kadai hukumomin lafiyar kasar ke fuskantar cikas ba, domin kuwa hatta al´ummar kasar ma akwai bukatar wayar musu da kai kan wannan sabon tsari na amfani da fasahar zamani a bangaren harkokin kiwon lafiya. Hukumomin dai sun tsaya kai da fata cewar wannan wani abu ne mai matukar muhimmanci ga rayuwar al´ummar Ghana kasancewar za a saukaka jigila da ma zirga-zirgar kayayyakin kiwon lafiya da ma jini don isar wa ga mutanen da ke cikin surkukin wuri mai wuyar futsawa.

 

Sauti da bidiyo akan labarin