Ghana: Shekaru 400 da cinikin bayi
A shekarar 1619 jirgin farko ya tashi da bayi daga Ghana zuwa Amirka, shekarar 2019 ta kasance lokacin tuni da ranar da aka yi wa lakabi da "Year of Return" inda ake kira ga 'yan asalin Ghana da ke waje da su dawo gida.
Fada da magabata
Mai shekaru 50 da haihuwa, Abdul Sumud Shaibu yana nuna hoton kakansa a wayar salula. Ya ce ''kalli tsayinsa'' kakanni na, dogaye ne kuma karfafa, wasunsu, sun yaki masu safarar bayi inji Shu'aibu, akwai lokacin da shakka babu suka yi nasara akwai kuma lokacin da suka yi rashin nasara, rashin na nufin rayuwa cikin kangin bauta.
Kan hanyar zuwa kasar Portugal
Dama sana'ar bayi na bunkasa a yankin yammancin Afirka kafin ma jirgin bayin farko ya isa Amirka. A karshen karni na 15, jirgin ruwan kasar Portugal na safarar bayi daga Afrika zuwa kasar. A lokacin ana da Turawa da yawa da ke zaune a can, wannan ya kara bunkasa sana'ar cinikin bayi daga yammancin Afirka ya zuwa kasar Amirka.
Musayar bayi a tsakanin yankunan Atlantic
Ana kiran tsarin da abin da Bahaushe ke cewa ''bani gishiri na baka manda'' akasarin Turawan za su kawo makamai da kayayyakin masarufi a kuma biyasu da bayi. Za a dauko bayin daga Afirka zuwa Amirka, a gaba a kuma sake musayar bayin da kayan sha kamar gahawa ko ganyen shayi, wadannan kayayyakin za a kuma mayar da su kasashen nahiyar Turai.
Tsaka mai wuya
Halin da bayin ke tsintar kansu a yayin bulaguron ketarawa da su tekun Atlantic, daidai yake da na dabbobi, ana jera bayin daya kan daya kafin a garkamesu da karafuna, babu ishashen abinci ko ruwan sha, wanda ya gamu da rashin lafiya kuwa, ana daukarsa a jefa shi cikin teku don hana yaduwar cutar a tsakanin sauran bayin.
Bauta a gonar auduga
Bayan sun isa, a ''sabuwar rayuwar'' da suka sami kai ciki, ana tilasta wa bayin aikin karfi na noman auduga da rake. Masu gonakin attajirai ne a yayin da bayin za su ci gaba da kasancewa cikin tsananin talauci. Baya ga haka, rayuwarsu bata ingantuwa face azaba da muzgunawa da ake yi musu. Akwai wadanda ake kai wa aiki a masana'antar hakar ma'adinai, cin zarafi, ba sabon abu ba ne a garesu.
Azaba
Ga akasarin bayi, azabtarwa, ta zame musu jiki, ana zane su ko ladabtar da su ta hanyar yaba musu karfe mai zafi da ke barin tabo a jikinsu. Iyayen gidansu ne ke da ikon ba su izinin aure. Bayi ba su da ta cewa, ba su kuma da izinin samun 'yanci daga iyayen gidansu. Wannan karfen da ake gani, an yi amfani da irinsa don garkame bayi, yana dakin adana tarihi na kasar Ivory Coast.
Akasarin bayin sun fito ne daga kasashen yankin yammancin Afirka
Cinikin bayin ya kai kololuwa a karni na 18. Kashi biyu daga cikin uku na bayin da aka kai Amirka, sun fito ne daga kasashen yankin Afirka ta yamma, kamar yadda aka nuna a hoton da ke sama. Za a ga daga tashashin jiragen ruwan da aka yi safarar su zuwa Amirka. Ba a iya tantance adadin bayin da aka sayar ba, amma ana zaton mutum miliyan arba'in aka sayar a matsayin bayi.
Masu cinikin bayi na Jamus
Jagoran Brandenburg, Friedrich Wilhelm, shi ya gina katafariyar cibiyar ''Friedrichsburg" a gabar ruwan kasar Ghana. A zamanin cinikin bayin, ana kiran kasar da suna "Gold Coast". Daga can ne, Brandenburgers, ya tsunduma cinikayya ta musayar bayin na yankin Atlantic, bayi kusan dubu dari uku aka kiyasta an yi safararsu zuwa abin da a wancan lokacin ake kira da sabuwar rayuwa.
Tunawa da mamata
A Adidwan, wani kauye da ke yankin Ashanti, Nana Assenso, ya kai ziyara kabarin kawunsa Kwame Badu. An rada masa sunan wani kakansu da aka sayar a lokacin cinikin bayi. Tun wancan lokacin, ake ci gaba da rada wannan suna daga zamani zuwa zamani na 'ya'ya zuwa jikoki. Nana Assenso shi ma yana da yaron da aka radawa suna Kwame Badu.
Wurin adana tarihi na Nuhalenya Ada
Fitaccen mai zane na kasar Ghana Kwame Akoto Bamfo, ya kamanta magabata da aka sayar kamar yadda yake yanzu haka a dakin adana tarihi a kauyen Nuhalenya Ada. Duk da cewa Britaniya ta ayyana dokar haramta cinikin bayi a shekarar 1808 aka kuma amince da dokar a hukumance a shekarar 1815 a Viennan, ba a daina ba har sai shekarar 1870. Ghana na ci gaba da tuni da zamanin safarar bayi a gabar ruwanta.