Ghana: Sana′ar noman Kashu | Himma dai Matasa | DW | 03.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Ghana: Sana'ar noman Kashu

Manoma a Ghana sun raja'a kan noman Kashu wanda masana ke hasashen nan da wani lokaci zai iya danne Cocoa ta fanni samarwa kasar kudaden shiga.

Yanzu haka 'yan kasuwa daga kasar India su ne ke kayyade wa farashin kashun. Wannan ya sa manoman ke kokarin ganin cewar gwamnati ta shigo cikin lamarin kamar yadda ta yi wa cocoa.

Lokacin faduwar rana a Ghana wannan lokacin ne manoman kasar ke kokarin shigar da Kashu din da noma cikin rumbu. Wani Dattijo mai kimanin shekaru 70 da ya kwashe shekaru da dama yana noman kashu a kasar yace.

Da wannan Noman na Kashu ya dauki nauyin Iyalansa kama daga ci, sha, harma da ilimi 'ya'yansa. Dattijon ya ce banda haka ma har kudin kashewa yake samu.

Ita ma wata mata mai suna Edna Kudalo wadda 'yar asalin kasar ta Ghana da ke da kamfanin sarrafa kayan marmari ta damu kwarai kan yadda lemon kasashen waje ya mamaye kasuwar kasar.

Kashi tamanin cikin dari na Lemon da ake sha a kasar nan ana shigo da su ne daga Ketare, matukar za'a bamu dama musamar da koda kashi hamshin cikin dari ne na lemon da ake bukata da mu samar da aikin yi ga jama'a. Domin mafiyawan Lemon da ake kawo mana bawai na kwarai bane. In har aka bamu dama to kuwa zamu yi iya kokarin mu muyi lemo da asalin kayan marmari. Ta yadda zamu bunga kasa kamfanonin mu.

Kasar Ghana dai bayan kashu tana samar da kayan marmari nau'i daban daban. Kuma daga cikin matsalolin da manoman suke fuskanta bayan riba ga masayi, a kwai batun magungunan feshi, wutar daji da sauran matsaloli da ke barazana ga Noman na kashu.