Ghana: Rejistan masu zabe da corona | Siyasa | DW | 07.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ghana: Rejistan masu zabe da corona

An kammala zagaye na farko na rejistan masu kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki na Ghana da aka shirya guddanarwa a karshen wannan shekara.

A cibiyoyin yin rejistan da wakiliyar DW ta ziyarta babu barin tazarar mita biyu tsakanin juna kamar yadda hukumar lafiya ta bukaci a yi a wajen rejistan zaben. Hukumar zaben ta ce za ta tabbatar cewar duk mai dauke da annobar Covid-19 ba zai kawo jiki a rufunan yin rejistan ba.

Bulo da tsarin rage cunkoso a wurin rejistan


Dangane da halin da duniya ta tsinci kai a ciki yanzu haka na fama da annobar Covid-19, hukumar zaben Ghana ta bulo da wani tsari na rage cunkoso jama'a da ke zuwa yin rejistan. Da wannan sabon tsarin hukumar zabe a duk rana na ba da kati ga mutanen da aka kayade za su iya yin rejistan. Wadanda ba su da wannan kati kuwa ba za su iya shiga gurin yin rejistan ba.

Kai ruwa rana tsakanin hukumar zabe da jam'iyyun siyasar kafin soma yin rejistan zaben


Tun farko dai an yi ta samu sabanin tsakanin 'yan siyasar na adawa da kuma hukumar zaben wanda suka shigar da kara a gaban kotun tsarin mulki a game da tsarin da hukumar zaben ta fitar. Na cewar takardar haifuwa da sauran takardu ba su isa a yi rejistan da su ba sai da fasfo ko takardar shaidar zaman dan kasa abin da kotun ta tabbatar da shi ta kuma yi watsi da koken 'yam adawar.