Ghana na neman tallafin IMF | Labarai | DW | 04.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ghana na neman tallafin IMF

Gwamnatin Ghana ta nemi taimakon Hukumar Tsara Kuɗaɗe ta Majalisar Ɗuniya IMF domin dakatar da faɗuwar darajar takardar kuɗin ƙasar wato Cedi.

Shugaban ƙasar na Ghana John Mahama Dramani wanda ya bayyana haka a taron Amirka da ƙasashen Afirka da ake gudanarwa a Washington. Ya ce ƙasarsa na buƙatar tallafin na hukukomin kuɗin na duniya domin daidaita shirin tsuke bakin aljihun gwamnatin.

Darajar takardar kuɗin Cedin, ta faɗi warwas da kishi 40 cikin ɗari ƙasa ƙwarai ga kuɗin Amirka idan aka yi canji. Yazuwa yanzu Ghana ita ce ƙasa ta biyu a cikin ƙasashen Afirka da ta nemi agaji Hukumar ta IMF bayan Zambiya wacce ta gabatar da buƙatar a cikin watan Yuni da ya gabata.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal