Ghana: Mutane 22 sun mutu wajen ginar zinari | Labarai | DW | 07.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ghana: Mutane 22 sun mutu wajen ginar zinari

'Yan sanda a Ghana sun ce addadin mutanen da suka mutu a cikin wata mahakar zinari ta bayan fage a kudu maso yammacin kasar sun haura daga 17 zuwa 22.

Mahakar mai zurfin mita 80 wacce aka daina aiki da ita wadda kuma gwamntin ta haramta a farkon wannan shekara ta rubta da masu ginan zinarin a ranar Lahadin da ta gabata. Ghana dai ita ce kasa ta biyu a Afirka bayan Afirka ta Kudu wadda da ke da  arzikin karfen zinari, sai dai a karo da dama a kan samu irin wannan hadari.