1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Gwamnati ta nemi afuwar 'yan kasa

Ahmed Salisu
November 18, 2022

Ministan kudin Ghana Ken Ofori-Atta ya nemi afuwar 'yan kasar a wannan Juma'ar kan irin matsin tattalin arziki da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

https://p.dw.com/p/4Jke6
ECOWAS Westafrikanische Staaten verhängen Sanktionen gegen Mali und Guinea
Shugaban Ghana Nana Akufo-AddoHoto: Nipah Dennis/AFP

Ministan ya nemi afuwar 'yan kasar ce a lokacin da ya bayyana gaban wani kwamiti na majalisar dokokin kasar da ke gudanar da bincike a kansa da kuma irin aikin da ya gudanarwa.

Kasar ta Ghana dai a dan tsakanin nan ta fada cikin masassarar tattalin arziki inda farashin kayayyaki musamman ma na masarufi ya yi tashin gwaron zabi, lamarin da ya sanya 'yan kasar kokawa har ma suka nemi da a sallami ministan daga bakin aikin yayin da wasu 'yan kasar ke neman gwamnatin Shugaba Nana Akuffo Ado ta yi murubus.