1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: An fara yi wa dalibai rajistar zabe

July 10, 2020

Hukumar zaben kasar Ghana ta fara yi wa dalibai da suka kai munzalin yin zabe rajistar katin zabe, inda ta baza jami’anta a makarantu kusan 700 domin gudanar da wannan aikin rajistar.

https://p.dw.com/p/3f8fG
Ghana Präsidentschaftswahl 2016 - Auszählung der Stimmzettel
Hoto: DW/K. Gänsler

Kaddamar da aikin rajistar ya biyo bayan wani zama da aka yi tsakanin wakilan jam’iyyun siyasa da hukumar zabe EC, a ranar 9 ga watan nan na Yuli. Za a yi wa dalibai wadanda suka cika shekaru 18 ko fiye domin basu damar kada kuri’a a zabbukan da ke gabatowa na watan Disamba. Daraktar gudanar da harkokin zaben, Dr Serebour Quaicoe, ya ce sun dauki wannan mataki ne bisa amincewar ma‘aikatar Ilimi ta kasa.

Ghana Wahlen Abstimmung Auszaehlung Warten
Rajistar masu zabe a kasar GhanaHoto: AP

“Mun samu wasika daga ma’aikatar ilmi ta Ghana da ke cewa yara baza su tafi gida ba, kuma ba za’a iya kai musu ziyara ba kuma dama wasu makarantun na gudanar da wannan aiki a saboda haka babu wata matsala, kuma za a gudanar da aikin tare da kiyaye matakan kariya da aka saba.

A yayinda jam’iyyar NPP mai mulkin kasar tayi na’am da shawarar dari bisa dari, a waje guda kuma ya janyo tsokaci daga jama’a cewa  dama gwamnati ta mayar da yara makarantu ne don zabe amma ba dan jarabawarsu ba. Inda a cikin bayaninsa wani tsohon jami’ain jam’iyyar mai hada kan matasa na kasa ya baiyana.

Mädchenschule in Kumbungu Ghana
'Yan mata daliban makaranta a kasar GhanaHoto: DW/M. Suuk

“Idan bamu basu damar yin rajista a makarantu ba, hakan na nufin dole sai sun yi shi a waje, wanda zai jefa su cikin hadarin kamuwa da cutar corona“.

Majalisar malluma dana iyayen dalibai PTA a takaice sun yi Allah wadai da matakin ta bakin shugaban kungiyar Alexander Yaw Danso.

“A lokacin da za’a bude makarantu babu wanda ya fada mana cewa za’a yi wa yara rajisata a makarantunsu, kuma bana tunanin wani matakin da zamu dauka a yanzu zai yi wani tasiri domin an riga an fara, kuma hakan bai dace ba“.

A nata bangaren jam’iyyar NDC, dake zaman babbar jam’iyyar adawa ta ce da walakin goro a miya.