Ghana: Amfani da dabarar makamashin hasken rana wajen kasuwanci
Salon rayuwa
March 25, 2020
Farashin makamashi a Ghana ya fi ko ina tsada a yammacin Afirka. Sai dai yanzu wata kungiyar farar hula na koya wa yara matasa yadda za su yi amfani da fasahar makamashin solar don kasuwanci tare da rage dogaro a kan kamfanonin wutar lantarki da suka yi kaka-gida.