Germain Katanga zai fito daga kurku | Labarai | DW | 18.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Germain Katanga zai fito daga kurku

Gwamnatin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango ta ce za ta ci gaba da tuhumar tsohon jagoran 'yan tawayen na Ituri na Ƙungiyar FRPI Germain Katanga.

Germain Katanga wanda ake kira da sunan simba watau zaki da harshen Swahili,a shekarun 2014 kotun ƙasa da ƙasa da ke hukunta miyagun laifukan yaki ICC.Ta yanke masa hukucin ɗaurin shekaru 12 na zaman gidan yari saboda samunsa da hadin baki a harin da aka kai a wani ƙauyen da ke yankin arewa maso gabashin Kwango wanda a ciki mutane ɗari biyu suka mutu.

An dai kamashi tun a shekarun 2003,kuma a ƙarshe kotun ta ICC ta mayar da shi zuwa Kwango domin ya kammala zamansa na gidan kurku.Yau Litinin yakamata Germain Katanga ya fito daga gidan kukrkun,to sai dai gwamnatin Kwangon ta ce za ta sake tuhumarshi da laifin kisan wasu sojoji MDD a Ituri a shekarun 2005.