George Weah ya sha rantsuwar kama aiki
January 22, 2018Talla
Rantsuwar dai ta gudana ne gaban dubban magoya bayansa da manyan baki musamman ma shugabannin kasashe daga sassan duniya daban-daban. Wannan dai shi ne karon farko tun shekarar 1944 da wata gwamnatin farar hula ta mika mulki ga 'yar uwarta ta farar hula bayan da Weah din ya karbi mulki daga hannun tsohuwar shugabar kasar Ellen Johnson-Sirleaf wadda ta shafe shekaru 12 ta na jan ragamar kasar.