1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gaza: Israila ta hallaka kwamandan Hamas

Abdullahi Tanko Bala
November 12, 2018

Wani farki da sojin Israila suka kaddamar a Gaza ya haddasa hasarar rayuka da suka hada da kwamandan Hamas da kuma wani sojin Israilar

https://p.dw.com/p/38526
Gazastreifen Khan Youni Getötete Hamas Mitglieder
Hoto: Getty Images/AFP/S. Khatib

Sojin Israila sun hallaka wani babban kwamandan Hamas tare da wasu yayan kungiyar su biyar yayin wani farmaki da suka kaddamar a yankin zirin Gaza a ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce wani sojin Israila daya ya rasa ransa yayin da rikici tsakanin bangarorin biyu ke neman kara ta'azzara.

Hamas ta ce sojin kundunbala na Israila sun kutsa kai yankin na zirin Gaza kusa da Khan Yunus inda suka harbe Nour Baraka mukaddashin kwamnadan dakarun kungiyar.

A cikin wata sanarwa Hamas ta ci alwashin daukar fansa lamarin da ya sojin Israilar kaddamar da wasu hare hare ta sama.

Ministan tsaron Israila Avidgor Lieberman ya gudanar da taro da manyan hafsoshin sojin kasar domin nazarin yanayin da ake ciki na tsaro.