1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar wasan kwallon Tennis

Suleiman Babayo
March 20, 2018

Shahararren dan wasan na duniya, Roger Federer ya ci gaba da rike matsayi na daya na wanda ya fi shahara a fagen wasan kwallon Tennis, kamar yadda hukumar kula da gasar ta tabbatar a wannan Litinin

https://p.dw.com/p/2ud2O
Tennis US Open 2017 Roger Federer
Hoto: Reuters/USA Today Sports/J. Lai

Haka na zuwa duk da rashin nasara da Federer ya yi lokacin wasan karshen na Indian Wells yayin karawa da Juan Martin del Potro. Kuma wannan ke zama rashin nasara na farko ga Federer dan kasar Switzerland cikin wannan shekara ta 2018. A matsayi na biyu akwai Rafael Nadal dan kasar Spain.

A bangaren mata Simona Halep 'yar kasar Romaniya ta shiga gaba a matsayi na farko. Wani abun mamaki shi ne Naomi Osaka da ta samu nasara yayin gasar karshe na Indian Wells tana matsayi na 22 bisa gwanancewa a gasar na tennis na mata.

(2) Caroline Wozniacki, Denmark, 7,430 3.

(3) Garbine Muguruza, Spain, 5,970 4.

(4) Elina Svitolina, Ukraine, 5,425 5.

(8) Venus Williams, Amurka, 4,452 9. (9)