1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: Qatar 2022

Suleiman Babayo LMJ
November 28, 2022

Faransa ta zama kasa ta farko da ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya kana mai masaukin baki Katar ta zama ta farko da aka fitar, inda Kanada ta zama ta biyu da aka cire.

https://p.dw.com/p/4KC9a
Katar | Kameru | Sabiya | Maxim Choupo-Moting
Kamaru ta yi kunnen doki, abin da ya sa take da sauran fataHoto: Frank Augstein/AP Photo/picture alliance

Yayin da aka shiga zagaye na biyu na gasar a wasan da aka kammala tsakanin Kamaru da Sabiya an tashi an tashi canjaras uku da uku, abin da ke nuna lallai Kamaru na bukatar samun nasara a karawarta da Brazil kafin tsallakawa zuwa mataki na gaba kasancewar ta sha kaye a wasan farko a hannun kasar Switzerland da ci daya mai ban haushi. Kasar Katar mai masaukin baki ta zama ta farko da aka cire daga gasar ta neman cin kofin kwallon kafar duniya, bayan Senegal ta doke ta da ci uku dadaya. A wasansu na farko dai Katar din ta sha kaye a hannun Ekwado da ci biyu da nema. Ita ma Kanada an cire ta, bayan Beljiyam ta doke ta da ci daya mai ban haushi a wasan farko, kana Kuroshiya ta doke ta da ci hudu da daya a wasansu na biyu.

Katar 2022 | Faransa | Ostireliya
Faransa ce kasa ta farko da ta samu nasarar kai wa zagaye na gabaHoto: Nigel Keene/Pro Sports Images/IMAGO

Kasar Faransa ta tsallaka zuwa zagaye na biyu da ake bukatar kasashe 16 da za su kai wannan mataki, bayan ta samu nasarar doke Denmak da ci biyu da daya kuma a wasanta na farko ta doke Ostreliya da ci hudu da daya. Koda yake bayan da ta sha kashi a hannun Faransa, Ostreliyan ta zage damtse, inda ta lallasa Tunisiya da ci daya  mai ban haushi, abin da ka iya ba ta damar karawa a zagaye na kungiyoyi 16 da ba ta taba kai wa ba a tarihin kwallon kafarta. Jamus kuwa da ta lashe kofin kwalon kafa na duniyar har sau hudu na bukatar yin nasara a wasanta na gaba, kafin ta samu sararin tsallewa. Kasar ta tashi kunne doki daya da daya a fafatawarsu da Spain, inda a wasan farko Japan ta doke ta da ci biyu da daya. Ita ma Japan din ta sha kaye a hannun Kwasta Rika da ci daya mai ban haushi.

Katar 2022 | Koriya ta Kudu | Ghana
'Yan wasan Ghana sun lallasa Koriya ta Kudu da ci uku da biyuHoto: Stuart Franklin/REUTERS

Su ma dai kasashen Afirka sun fara taka rawa kadaran-kadahan, inda Moroko ta samu nasara a kan Beljiyam da ci biyu da nema, abin da ya janyo tsallen murna ga kasar wadda ta shafe shekara da shekaru tana jiran irin wannan nasara a gasar neman cin kofin kwallon kafa na duniyar. Beljiyam dai, na cikin jiga-jigan kasashen da ake ganin za su taka rawa a gasar. Senegal ma ta farfado bayan samun nasarar doke mai masaukin baki Katar da ci uku da daya, bayan ta sha kaye a hannun Switzerland a wasan farko ci daya mai ban haushi. Ghana ma ta huce haushinta a kan Koriya ta Kudu da ci uku da biyu, bayan da a wasan farko Potugal ta caskara ta ita ma da ci uku da biyu. Kasashe da dama dai suna kan siradi, inda wasan karshe na matakin rukuni zai tantance makomarsu.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani