Garkuwa da ′yan majalisa a Banizuwela | Labarai | DW | 06.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garkuwa da 'yan majalisa a Banizuwela

A Benizuwela 'yan majalisar dokokin bakwai ne suka ji rauni a lokacin da wasu daruruwan magoya bayan Shugaba Nicolas Maduro suka yi garkuwa da 'yan majalisar da ma 'yan jarida a tsawon awoyi tara. 

A Banizuwela 'yan majalisar dokokin bakwai da wasu ma'aikatan majalisar kasar kimanin 10 ne suka ji rauni a lokacin da wasu daruruwan magoya bayan Shugaba Nicolas Maduro dauke da kulake da wukake da kuma duwarwatsu suka kutsa da karfi a cikin ginin majalisar wacce 'yan adawa ke da rinjaye a cikinta tare da yin garkuwa da 'yan majalisar da ma 'yan jarida a tsawon awoyi tara. 

Sai a cikin daren jiya ne jami'an 'yan sanda dauke da kayansu na sulke sun kutsa a cikin majalisar inda suka yi nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su daga hannun masu zanga-zangar. Sai dai kuma Shugaba Nicolas Maduro ya nisanta kansa da mutanen da suka yi garkuwa da 'yan majalisar yana mai cewa ba shi da hannu ko miskala zarratun a cikin lamarin tare ma da yin Allah wadai da shi.

Watanni da dama kenan da masu adawa da milkin shugaba Nicolas Maduro ke gudanar da zanga-zangar neman tilasta masa yin murabus daga kan mukaminsa na shugabancin kasar a bisa zarginsa da yi wa kundin tsarin mulkin kasar karan tsaye da kuma kasa shawo kan matsalolin tattalin arzikin da kasar ke fama da su a shekarun baya bayan nan.