Garkuwa da jama′a a yammacin Afirka | Labarai | DW | 16.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garkuwa da jama'a a yammacin Afirka

Kamfanin Dillancin Labaran Mauritaniya ya ce ya samu bidiyon da alQa'ida ke tsare da wasu 'yan yammacin duniya.

Kamfanin Dillancin Labaran Mauritaniya ya ce ya samu fei-fei bidiyon da kungiyar alQa'ida, reshen arewacin Afirka ta fitar, inda a ciki take nuna mutane bakwai - 'yan kasashen yammacin duniya da take ci gaba da yin garkuwa dasu domin neman kudin fansa, bayan sacesu a yankin yammacin Afirka. Wadanda ake garkuwa da su din dai, sun hada da wasu Faransawa hudu da suka sace daga wani wurin hako ma'adinin Uranium a kasar Nijar, shekaru uku kenan da suka gabata. Sai kuma wani dan kasar Holland da Sweden da kuma Afirka Ta kudu da suka sace daga birnin Timbuktu na kasar Mali a cikin watan Nuwamban shekara ta 2011. Daniel Larribe, wanda ya gabatar da kansa a matsayin jagorar Faransawa a cikin fei-fei bidiyon, ya ce kungiyar alQa'ida reshen maghrib, da a ka fi sani da suna AQIM ce ta sacesu daga garin Arlit na jamhuriyar Nijar a ranar 16 ga watan Satumban shekara ta 2010. Kamfanin dillancin labaran dai, ya ruwaito cewar, Larribe yana magana ne a ranar 27 ga watan Yuli, kana ya ce yana cikin koshin lafiya, duk da cewar ya fuskanci barazanar kissa, yana mai cewar, duk wai abin da ya faru dashi, to, kuwa gwamnatin Faransa ce zai dora wa alhakin hakan.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman