Garkuwa da Baki a arewacin Najeriya | Siyasa | DW | 17.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Garkuwa da Baki a arewacin Najeriya

'Yan bindiga sun yi garkuwa da 'yan kasashen ketere a garin Jama'are cikin Jihar Bauchi ta Najeriya

'Yan bindiga sun yi garkuwa da 'yan kasashen ketere bakwai, a garin Jama'are da ke Jihar Bauchi, a yankin arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya.

Babban jami'in 'yan sandan jihar Mohammed Ladan ya tabbatar da faruwan lamarin. 'Yan sanda sun ce 'yan bindigan sun yi garkuwa da 'yan kasar Lebanon hudu, daya dan Birtaniya, dan Italiya, sannan dayan dan Girka. 'Yan sanda sun ce lamarin ya faru da sanyin safiyar wannan Lahadi (17.02.2013).

Yankin arewacin kasar ta Najeriya ya fuskancin matsalolin tsaron cikin shekarun da su ka gabata, abun da ya janyo mutuwan dubban mutane cikin hare haren 'yan bindiga da ake dangantawa da kungiyar Boko Haram mai gwagwarmaya da makamai.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin