Garkuwa bisa dalilan siyasa a Libiya | Labarai | DW | 18.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garkuwa bisa dalilan siyasa a Libiya

Sace-sacen manyan jami'an gwamnati na neman zama ruwan dare a Libiya inda a karo na biyu cikin watanni biyu, aka sake sace wani mai rike da babban mukami a kasar.

Wasu 'yan bindiga a kasar Libiya da ba a kai ga sanin ko su wanene ba sun sace mataimakin shugaban hukumar leken asirin kasar Mustafa Noah, wanda ba ya tare da jami'an tsaro dake yi masa rakiya a lokacin da aka sace shin, a wajen Filin sauka da tashin jiragen sama na Tripoli bayan dawowarsa daga bulaguro a kasashen ketare. Kawo yanzu babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin sace shin ba, sannan ba a kai ga sanin inda ya ke ba.

Idan dai za a iya tunawa a watan Oktoban da ya gabata ne wasu 'yan bindiga suka sace firaminstan kasar Ali Zaidan, kafin daga bisani su sako shi bayan da aka kwashe tsahon wasu sa'oi. Shugabanni a Tripoli babban birnin kasar sun bukaci da a shiga wani yajin aiki na gama gari domin tilastawa gwamnatin kasar kan ta dakile ayyukan 'yan bindiga na sa kai, da ake dorawa alhakin rikicin da ya faru a makon jiya da yayi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 46.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe