Garin Goma ya koma hanun gwamnati | Labarai | DW | 04.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garin Goma ya koma hanun gwamnati

Gwamnatin ƙasar Jamhuriyar Demokaraɗiyyar Kongo ta sake kafa iko a garin Goma na gabashin ƙasar.

Gwamnatin ƙasar Jamhuriyar Demokaraɗiyyar Kongo ta sake kafa iko a garin Goma da ke gabashin ƙasar, bayan kammala janyewar 'yan tawaye a wannan Litinin da ta gabata.

Jami'an gwamnati da sojoji sun sake komawa wuraren da su ke gudanar da aikin cikin yankin gabashin ƙasar, bayan kwanaki 11 da garin ya kwashe hannun 'yan tawaye. Gwamnan Jihar na Arewacin Kivu Julien Paluku na cikin waɗanda su ka koma, da kuma ministan cikin gida Richard Muyej, wanda ke saka ido kan komawar hukumomin gwamnati bakin aiki.

Wani rahoton ƙwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, 'yan tawaye ƙungiyar M23 sun haɗa da sojojin ƙasar Rwanda, yayin da ƙasar Uganda ke bada taimakon kayan aiki ga 'yan tawayen.

Tuni aka miƙa wasiƙar da ke tabbatar da haka ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Shugaban ƙasar ta Jamhuriyar Demokaraɗiyyar Kongo Joseph Kaliba ya yi alƙawarin sauraron buƙatun 'yan tawayen.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi