Gargadi ga Yukren game da rigingimu a kasar | Labarai | DW | 22.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gargadi ga Yukren game da rigingimu a kasar

Tarayar Turai ta yi barazanar daukar mataki akan gwamnatin Yukren dangane da tsauraran matakan da take dauka akan 'yan adawa.

Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso, ya bayyana cewar, Kungiyar Tarayyar Turai na duba yiwuwar daukar mataki akan gwamnatin Yukren, bayan mutuwar akalla mutane biyu yayin boren nuna adawa da gwamnatin kasar, da kuma amincewa da dokokin da masu adawa suka ce na da nufi dakile masu bore ga gwamnati ne. Barroso, ya ce kungiyar na ci gaba da sanya ido dangane da yanda lamura ke tafiya a kasar, da kuma nazarin irin matakan da za ta dauka game da dangantakarta da hukumomin kasar ta Yukren. Akan hakane, shugaban hukumar, ya gabatar da kira na musamman ga hukumomin kasar ta Yukren da su hanzarta daukar matakan hana rincabewar rikicin, da kuma shiga tattaunawar samar da zaman lafiya tare da 'yan adawar kasar da kuma kungiyoyin kare fararen hula. Ya kuma bukaci sassan da ke rikicin da su daina tada rigima da kuma yin amfani da karfi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohamnmad Nasir Awal