1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gargaɗin Majalisar Ɗinkin Duniya ga Najeriya

March 14, 2014

Babbar jami'ar Hukumar kare hakkin bil 'adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta zanta da masu ruwa da tsakin ƙasar, inda ta buƙaci da a tabbatar an kamanta adalci wa kowa dan rage raɗaɗin hare-haren da suka addabi ƙasar

https://p.dw.com/p/1BQ7s
Navi Pillay
Hoto: Reuters

A wani abun dake zaman kama hanyar barin kasar hannu a rabbana, babbar jami'ar Hukumar kare hakkin bil 'adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya na shirin barin birnin Abuja ba tare da shawo kan mahukuntan kasar na mantawa da batun dokar hana auren jinsi a kasar ba.

Kama daga matsalar rashin tsaron dake iya wuya a sassa daban daban na tarrayar Najeriyar, ya zuwa 'yanci na tsirarrun da ya kunshi dokar hana auren jinsi dama makomar zabiyan kasar ya zuwa kokari na tabbatar da yancin yara kanana dama hali na 'yan kurkukun kasar dai ta kai ga tabo taiki ta kuma daki jaki, ga babbar kwamishinar kula da kare hakin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniyar dake kare wata ziyarar aiki ta kwanaki hudu a kasar.

Yaƙi da ta'addanci a Najeriya ya gagari kundila

Navi Pillay da ta share tsawon lokaci tana ganawa da jami'ai na gwamnati dama kungiyoyin dake zama da gindinsu cikin kasar dai ta kai ga yabo da rankwashi ga kokarin kasar na tabbatar da yancin kowa kama daga 'yan Boko Haram din da ta zarga da kisan ba gaira ya zuwa jami'an tsaron da tace sun wuce gona da iri dai kwamishinar dake kasar ta Najeriya a karon farko ta ce yakin ta'addancin kasar yayi muni yayi baki.

Flüchtlingscamp Menawo
Rikici ya tayar da mutane daga matsugunnensuHoto: DW/M. Kindzeka

“Kungiyar ta kai hari ga mutane saboda kawai addininsu ko kuma sana'arsu ta aiki, sun rufe idanuwansu wajen kisa da cin mutuncin da yawa. Sun kona coci coci da gidaje na mutane.asibitoci dama makarantu. Sun hallaka yara a cikin bacci, wasu yan kungiyar ma sun kai ga sace mata da yara kanana tare da yi musu fyade. Akalla mutane dubu 500 ne dai aka raba da muhallinsu cikin kasar ta Najeriya a yayin kuma da wasu kusan dubu 57 ke warwatse cikin kasashe na makwabta. An kai ga mantawa da batun noma abun kuma da yanzu haka ke barazana ga samar da abinci cikin yanki, duk dai sakamakon ta'addancin da kungiyar ta boko haram ta kai ga shukawa”

Ba a kai ga samun gwamnati ta sauya alƙiblarta ba kan tsiraru

Pillay dake kammala ziyarar tata a dai dai lokacin da rikicin ke kara kazancewa dai ta kuma juya kan jami'an tsaron dake yakin da kuma ta zarga da wuce gona da iri a kokari na kwantar da tarzomar dake zaman irinta mafi girma a shekara da shekaru.

“Mutane da yawa da na gana da su yayin wannan ziyara tawa sun tabbatar mun cewar jami'an tsaron kasar sun taka hakkin bi'adama a cikin yakin. Wannan kuma ya dada raba al'ummar da abun ya shafa da jami'an tsaron . Ya kuma taimaka wajen samun karin magoya baya ga kungiyar. Duk da cewar dai ba'a tabbatar da girman wannan cin zarafi ba, gwamnatin ta fihimci cewar hakan bashi da wani alfanu. Kuma babban mashawarcin tsaron kasar ya tabbatar mun cewar ana daukar matakan gyara a bisa wuce gona da irin.”

To sai dai kuma ko bayan yakin 'yancin na tsiraru ko dai yara zabiya na kasar kusan dubu 800 da basu karatu sakamkon banbancin fatarsu, ko kuma yaran da ake yiwa kallon maita ana kashe su a sashe na kudu maso kudancin kasar ko kuma masu sana'ar ludu da madigon dake fafutukar tabbatar da karshen dokar hana auren jinsi gudan da kasar ta kai ga kafawa a farkon shekarar da muke ciki.

Albinos in Liberia
Yara zabiya na bukatar kariya da tallafiHoto: DW/J.Kanubah

Dokar hana auren jinsi na karo da dokar ƙasa da ƙasa

Duk da cewar dai Pillay din na shirin barin birnin na Abuja ba tare da shawo kan mahukuntan kasar na sauya tunani kan dokar ba, babbar jami'ar ta ce Majalisar Dinkin Duniya ba ta da niyyar kaiwa ga mataki na tabbatar da tilashi ga gwamnatin da ta ce ta karya dokoki da tanaje tanajen kasa da kasa, sannan kuma na barazana ga lafiyar yan ludun

“Majalisar dinkin duniya bata da niyyar daukar wani mataki kan wannan doka sai dai baiyyana damuwarta kai. Kuma kasa da kasa dama sauran kasashe sun yi Allah wadarar da ita kuma suna da dalilansu na yin hakan. A yayin da na iso Najeriya na lura cewar kunyi hakuri da masu wannan sana'a na lokaci mai tsawo, babu hukunci kan yan ludu da madigo a kasar na lokaci mai tsawo. Duk da cewar kuna da dokokin da suka haramta auren jinsi guda.

Na samu tabbaci daga ministan shari'a cewar wannan doka bata da laifin dora laifi saboda kawai tsari na sha'awar soyayyar dake cikin zuciya. Saboda haka akwai abubuwa guda biyu masu kyau, babu hukunci kan yan ludu, sannan kuma za'a ci gaba da mutunta damarsu ta sha'awar soyayya”

To sai dai kuma jami'ar ta kai ga yabon kasar da tace ta kara yawan wakilcin mata a cikin mulki, da kuma alakawarin mahukuntan kasar na tunkarar cin hanci.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Pinaɗo Abdu Waba