Garanbawul a gwamnatin Afirka ta Kudu | Labarai | DW | 17.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garanbawul a gwamnatin Afirka ta Kudu

Shugaban Jakob Zuma na Afirka ta Kudu ya gudanar da wani dan karamin garan bawul ga gwamnatinsa a wannan Talata inda ya tsige ministan ma'aikatar ilimi mai zurfi Blade Nzimande daga cikin gwamnatinsa. 

Ministan wanda mamba ne a jam'iyyar kwaminisanci ta SACP abokiyar kawancan jam'iyyar ANC ya yi kaurin suna wajen caccakar Shugaba Zuma a watannin baya bayan nan dangane da batun cin hancin da ake zarginsa da aikatawa. 

Tuni dai wannan mataki ya fuskanci suka daga jam'iyyar ta SACP da ma jam'iyyar ANC. Baya ga korar ministan ilimin Shugaba Zuma ya kuma canza wa ministan tsaro na kasar David Mahlobo mukami zuwa na ministan makamashi, nadin da ya sake farfado da muhawarar da ake a kasar a game da aniyar shugaba Zuma ta neman gina tashar makamashin nukiliya a kasar.