1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin zaman lafiya na matasa a Mali

Abdoulaye Mamane Amadou
November 28, 2019

A kasar Mali daruruwan matasa sun gudanar da tattaunawar zaman lafiya tsakanin kabilu daban daban na kasar a birnin Bamakon domin zama tsintsiya madaurinki daya.

https://p.dw.com/p/3TtO0
Mali, Bamako: Unterstützer des Präsidenten Ibrahim Boubacar Keita
Hoto: Getty Images/AFP/A. Risemberg

Taron na daruruwan matasan daga kabilu da dama wadanda galibinsu basa ga maciji da juna na zuwa ne a daidai lokacin da rashin jituwa tsakanin kabilun da kuma ayyukan ta'addanci ke kara samun gindin zama a kasar.

Akalla fararen hula fiye da 900 suka gamu da ajalinsu sakamakon rigingimu masu nasaba da kabilanci kamar yadda hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta sanar a cikin wani rahoto.

Elisabeth Arama daya ce daga cikin matasan da suka halarci taron daga yankin Mopti mai fama da rikici a tsakiyar Mali.

Fulani demonstrieren in Bamako, Mali
Hoto: AFP/Getty Images/A. Risemberg

 ‘’Ta ce a kullum idan dare ya yi muna kwana cikin fargabar yiwuwar kai mana hare-hare, matasan kauyenmu kan hada gwiwa domin yin sintiri daga karfe takwas na dare zuwa karfe hudu. Maharba kan yi mana rakiya idan har muna tafiya daga wani wurin zuwa wani domin kare lafiyarmu.’’

Ita ma wata matashiyar mai suna Fatoumata da ta fito daga kauyen Tenenkou na tsakiyar Mali na ganin duk da kasancewar jami'an tsaro a yankin da take bai hana su shiga cikin yanayi na fargaba ba.

Mali Proteste gegen Tuareg Angriffe Rebellen
Hoto: AP

 ‘’Ta ce duk da kasancewar jami'an tsaro a kauyenmu Tenenekou kusan ko da yaushe muna cike da fargaba, Akan samu 'yan ta'adda da ke satar jama'a a, ba mu da masaniya ko kashe su suke ko kuwa wani abin suke da su ba mu sani, amma kam muna cikin fargaba.’’

Mariama Guindo Maiga na daya daga cikin wadanda suka tsara taron na wayar da kan matasa, ta bayyana cewa matsalar tsaron da kasar Mali ke fama da ita na ci gaba da haddasa rudani da fargaba a tsakanin kabilun kasar,tana mai cewa fitowa fili a yi musayan bayanai tsakanin kabilun na da matukar muhimmanci.

An dai shirya taron ne karkashin jagorancin kungiyoyin farar hula masu zaman kansu da ke hankorin ganin kabilun kasar sun samu natsuwa da kwanciyar hankali a kasar ta Mali da ke fama da matsalolin tsaro barkatai.