Gangamin adawa da gwamnatin Banizuwala | Labarai | DW | 08.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gangamin adawa da gwamnatin Banizuwala

'Yan adawa sun nemi gudanar da gangami kasa baki daya har zuwa lokacin da za a kifar da gwamnatin Banizuwala ta Shugaba Nicolas Maduro.

'Yan adawa na kasar Banizuwala sun kira wani gaggarumin gangami domin kawar da Shugaba Nicolas Maduro daga madafun iko ta hanyoyin da suka hada da zaben raba gardama da kuma zanga-zanga. Masu adawa da gwamnati suna zargi kama karya da rashin mutunta dokoki kasa daga bangaren gwamnatin.

Tun cikin watan Disamba da 'yan adawa suka samu nasara yayin zaben 'yan majalisa aka fara takun saka tsakanin bangarorin biyu. Daga ranar Asabar mai zuwa 'yan adawa suke fara zanga-zangar, abin da ake gani zai iya jefa kasar ta Banizuwala da ke yankin Latin Amirka cikin sabon rikici na siyasa.