1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsi a wurin aikin ko na iyali na iya janyo damuwa

Zainab Mohammed Abubakar AH
December 6, 2019

Shirin Lafiya ari ya duba matsalar nan ta gajiyar kwakwalwa ko kuma Stress wadda kan jefa mutun cikin damuwa a wasu lokuta har ta janyo wata rashin lafiya.

https://p.dw.com/p/3UMMV
Künstliche Intelligenz und Kreativität
Hoto: Imago/Science Photo Library

Gajiyar kwakwalwa ko kuma stress, wanda ke janyo damuwa da makamantansu, abubuwa ne da mutum kan tsinci kansa a ciki wadanda ke da nasaba da matsaloli na matsin a rayuwa walau na iyali ko wurin aiki ko kuma kasuwanci, a wasu lokutan ma da rashin abin yi. Kwararru a fannin lafiya da likitoci sun bayyana matsalar gajiyar kwakwalwa da kan janyo damuwa, ta zama abu da ke da babban hadari ga lafiyar jikin bil Adama. To sai dai idan akace gajiyar kwakwalwa ko stress a turance me hakan ya ke nufi likitance, Dr Nasir Kabir Adakawa likita ne a Najeriya...