1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gabar tekun Guinea ta zama sabon sansanin 'yan fashin teku

December 21, 2012

Yayin da fashin jiragen ruwa ya ragu a Kahon Afirka, gabar tekun kasashen yammacin Afirka na barazanar zama wani yanki mai hatsari ga sufurin jiragen ruwa na kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/177lV
Hoto: picture-alliance/dpa

Sojoji da jiragen ruwan yaki da kasashen duniya suka girke a Gabar Tekun Somaliya dake a yankin kahon Afirka sun fara yin tasiri, inda a wannan shekara ta 2012 yawan fashin jiragen ruwa ya ragu matuka, idan aka kwatanta da shekarun baya. Sai dai a can yankin Gabar tekun Guinea dake yammacin Afirka wato Gulf of Guinea matsalar fashi a teku karuwa ta yi, inda alkalumman ofishin kula da sufurin jiragen ruwa dake birnin London suka nuna karin kashi 42 cikin 100 na fashi a tekun na Gulf of Guinea.

Kasashen dake gabar tekun Gulf of Guinea suna hako man fetir fiye da ganga miliyan uku a kowace rana. Nahiyar Turai na sayen kashi 40 cikin 100 na wanan mai yayin da Amirka ke sayen kashi 30 cikin 100. Shi yasa ba abin mamaki ba ne da gamaiyar kasa da kasa ke da sha'awar ganin an samu daidaituwar al'amura a tekun na Gulf of Guinea don yakar 'yan fashin teku.

Ba za a iya kwatanta Kahon Afirka da Gulf of Guinea ba

Sai dai a daura da yankin Kahon Afirka inda aka girke jiragen yaki masu yawa ciki har da guda tara daga tarayyar Turai a karkashin aikin da ake wa lakabi da Atalanta, masana na ba da shawara da a guji amfani da soji a tekun na Gulf of Guinea. Pottengal Mukunda daraktan ofishin kula da sufurin jiragen ruwa na kasa da kasa ya ce bai kamata a kwatanta halin da ake ciki a yankin Kahon Afirka da yankin Gulf of Guinea ba.

Piraterie Bildergalerie
Sojojin duniya ke tsaron gabar tekun SomaliyaHoto: picture-alliance/dpa

"Halin da ake ciki a gabar tekun Guinea ya bambamta da na Kahon Afirka, inda muke da kasa kamar Somaliya wadda ta durkushe. Amma dukkan kasashen dake gabar tekun Guinea suna da gwamnatoci da hukumomi dake aiwatar da dokoki. Sai dai suna bukatar isassun kayan aiki. Abu mafi kyau shi ne a tabbatar sun samu kayan aiki da suka dace sannan a matsa musu lamba su tinkari wannan matsala."

Shi ma Thierry Vircoulon na reshen kungiyar nan ta kasa da kasa dake bin diddigin rikice-rikice wato International Crisis Group, a birnin Nairobin Kenya, bai goyi da bayan girke sojojin kasashen duniya a gabar tekun Guinea ba.

"Kamata ya yi kasashen yankin Gulf of Guinea su dauki nauyin kula da tsaron yankin. Dole ne su karfafa hadin kai tsakaninsu. Sai dai a daya hannu a baiyane yake cewa wannan matsala ce ta masu aikata laifi da ke bukatar a dauki matakai dabam dabam don shawo kanta. Dole a yi gyara na tattalin arziki, a samar da guraben aiki ga jama'a."

Zaman kashe wando na daga cikin matsalolin fashin teku

Rashin aikin yi da tsadar rayuwa da kuma rashin adalci daga bangaren shugabanni na daga cikin dalilan dake sa matasa shiga fashin jiragen ruwa, inji Michael Strahl editan wata mujalla ta harkokin sufurin ruwa.

Aika-aikar 'yan fashin tekun na Somaliya da na Najeriya na da kammani. Suna amfani da kwale-kwalen masunta zuwa can cikin teku, sannan da zarar sun kusa da jirgin ruwan da suke son yi wa fashi, sai su canza zuwa kananan jiragen ruwa, su yi fashinsa zuwa wani yanki. Daga nan ne ake samun bambamci tsakanin 'yan fashin na Somaliya da na Najeriya, inji Strahl.

Piraterie Bildergalerie
Hoto: Elizabeth Kennedy/AP/dapd

"Yayin da akasari 'yan Somaliya ke neman kudin fansa kafin su saki jirgin da ma'aikatansa, su kuwa na yammacin Afirka suna wawashe kayan jirgin ne, musamman man fetir da ya dauko , su sayar a kasuwannin bayan fage."

Dukkan masanan sun yi ammanar cewa na ba da jimawa ba za a samu galaba a yakin da ake da 'yan fashin teku, kasancewa yanzu kasashe kamar Najeriya da Togo suna aiki tukuru don rage matsalar ta 'yan fashin ruwa.

Mawallafa: Rayna Breuer / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman