G5 Sahel: Fito na fito da ta'addanci
December 16, 2019Talla
A yayin wani babban taron kolinsu da suka kammala a birnin Yamai a yammacin jiya Lahadi (15-12-2019) Shugabannin sun bukaci tallafin kasashen na waje tare da kaddamar da wani gagarumin shiri kan nan zuwa shekaru biyu masu zuwa na kakkabe mayakan jihadin da suka samu gindin zama a yankunan kasashen Burkina Faso Mali da Jamhuriyar Nijar, a cewar sanarwarsu ta bayan taron.
taron na shugabannin na zuwa ne kwanaki bayan wani mumunan harin ta'addancin da ya afkawa sojan Jamhuriyar Nijar a garin Inates, da kuma ya hallaka sojan fiye da 70.