G20: An zanta kan ′yan gudun hijira da tsaro | BATUTUWA | DW | 08.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

G20: An zanta kan 'yan gudun hijira da tsaro

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi amfani da taron G20 wajen neman takwarorinta da su yi sassauci a kan batutuwa na cinikayya da sauyin yanayi da kuma na kwararar 'yan gudun hijira.

Taron na G20 da ke gudana a nan Jamus ya tabo batutuwa da dama ciki kuwa har da tsaro. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta  bukaci shugabannin kasashen da ke halartar taron da su kasance tsintsiya madaurinki daya wanda zai basu damar cimma burin da suka sanya a gaba inda ta ce "dukkanmu mun san manyan kalubalen da duniya ke fuskanta, mun kuma san lokaci na kurewa. Saboda haka za mu iya samun maslaha ne idan muka nuna shirin daidaita tsakaninmu kuma muka kusanci juna, ba tare da nuna taurin kai ba."

Deutschland Hamburg - G20 - Donald Trump und Vladimir Putin (Getty Images/AFP/S. Loeb)

Shugaban Putin na Rasha da Shugaban Amirka Donald Trump sun tattauna a wajen taron G20

Yayin wannan taro dai shugaban Amirka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun yi wata ganawa wadda ita ce irinta ta farko da suka yi a taro irin wannan. Trump ya fada wa Putin cewa haduwar da ya yi da shi wata dama ce ta kara inganta danganta tsakanin Amirka da Rasha inda ya kara da cewar "ni da Shugaba Putin mun sha tattaunawa kan abbubuwa da yawa kuma a ganina sun yi armashi. Muna sa ran samun abubuwa masu fa'ida ga Rasha da kuma Amirka da ma dukkan wadanda ke da ruwa a ciki."

To sai dai duk da cewar shugabannin sun nuna gamsuwa da haduwar da suka yi wajen wannan taro, a share guda zanga-zanga da aka riki yi ta ja hankali mutane da dama. A sassan birnin Hamburg inda nan ne ake taro, masu adawa da taron dai sun yi ta jerin gwano da zaman dirshen inda a wasu wuraren ma batun ya rikide zuwa tashin hankali har ma aka samu kone-kone sai dai 'yan sanda sun yi amfani da ruwan zafi da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa masu boren.

 

Sauti da bidiyo akan labarin