Fyade ya zama ruwan dare a Somaliya | Zamantakewa | DW | 21.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Fyade ya zama ruwan dare a Somaliya

A kasar Somaliya mai bin tsarin addinin musulunci tsantsa, magana kan abin da ya shafi fyade abune da aka haramta yinsa, ko da shike kasar na ci gaba da fama da wannan matsala.

A kasar Somalia mai bin tsarin addinin musulunci tsantsa, magana kan abin da ya shafi fyade abune da aka haramta yinsa, ko da shike matsalar ta fyade akwai alamun yanzu ta zama ruwan-dare a wannan kasa. Wadanda suka fi fama da wannan matsala kuwa sune mata da yan mata da kananan yara da suke nemi matsugunai a wasu yankuna na birnin Mogadishu, bayan sun tsere daga yankunan su na asali, sakamakon yaki ko yunwa.

A birnin na Mogadishu kadai irin wadannan korarru sun kai tsakanin dubu 200 zuwa dubu 370. Sojojin gwamnati da mayakan kungiyoyi masu dauke da makamai sukan biyo cikin dare su rika kwasar wadannan yan gudun hijira suna yadda suka so dasu ba tare da wani ya tsawata masu ba. Kungiyoyin kare hakkin mata suna iyakacin kokarinsu domin bada kariya da taimakawa wadnda suka tsira daga azabar fyaden da kuma karfafa masu gwiwar yiwa hukumomi bayanin abin da ya same su, yadda wadanda suka aikata laifin za'a rika hukuntasu.

Wata mace mai suna Sharifa Mohammed da ita ma tayi fama da wannan matsala ta fyade, tace har yanzu ta kasa gane dalilin da ya sanya wadannan sojoji da mayakan kungiyoyin masu dauke da makamai suka kama ta domin yi mata fyaden. Daga baya ta sami wurin zama a wani wuri da wata kungiyar kare hakkin mata mai suna kungiyar ceto matan Somalia, inda sai a canne ta sami karfin gwiwar fadin abin da ya same ta cikin dare watanni hudu da suka wuce:

"Tace lokacin da gari yayi duhu, wajejen karfe 10, na fita domin sayo abincin da yarana zasu ci, saboda mijina bai dawo da wuri ba ya kawo kudin da zan nemo abincin. Lokacin da na isa wani wurin sayar da abinci, sai ga wasu maza guda uku da suka tsaya a gaba na, suka ja ni da karfi zuwa wnai lungu mai duhu."

Straßenszene in Mogadischu Somalia

Somaliya ta rushe gaba dayanta

Lokacin da daya yake mata fyade, dayan ya riketa, daya kuma ya rufe mata baki. Ko da shike tayi kokarin gudu, amma sun fi karfinta, babu kuma wasu a kusa da zasu iya taimakonta, inda sai bayan misalin awa daya da rabi ne suka kyale ta tana kuka ta koma gida.

Wadannan mutane da sukai mata fyade, sun ji mata mummunan rauni, inda sai da tayi kwana da kwanaki bata fita ko ina. Mijinta ya tsaya kanta da taimako da goyon baya, abinda ba'a saba gani ba a kasashe da dama. Lokacin da matarsa ta isa gida, ya kuma gane abinda ya same ta, cikin fushi ya fita neman wadannan mutane ukku da sukai mata fyade. Shi kansa ko Sharifa basu yi tunain kai maganar wurin yan sanda ba, saboda bayan fiye da sekaru 20 na rashin gwamnati a Somalia, ba za'a ce akwai wata rundunar yan sanda ta kirki dake aiki a wannan kasa ba. Al'ummar Somalia ma basa daukar cewar akwai wata runduna ta yan sanda a kasarsu da zata iya kare jama'a, ko bin diddigi idan irin wannan laifi na fyade ya samu.

"Sharifa tace washegari na lura da mata guda ukku a sansaninmu, wadanda daga baya suka zo wurina suka tambayeni ko akwai wani abin da ya dame ni. Ko na gamsu da matakan tsaro a wannan wuri, ko akwai wani abin da ya faru cikin dare, ko kuma ina bukatar wani taimako."

Straßenszene in Mogadischu Somalia

Fyade ya yawaita a titunan Mogadishu

Wadannan mata guda ukku, ma'aikata ne na wata kungiyar agaji, wadda a wurinsu n Sharifa ta sami wurin zama yanzu. Kungiyar ta ceto matan Somalia, takan baiwa wadanda suka yi fama da matsalar fyade taimako ta hanyar magunguna da shari'a. Tun bayan da kungiyar ta bude wuraren taimako, mata akalla 11300 ne suka nemi taimako da agaji a fannoni dabam dabam a wannan wuri.

Mawallafi Kriesch/Umaru Aliyu
Edita: Mouhamadou Awal