1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

F.W.de Klerk ya rasu sakamakon ciwon daji

Abdullahi Tanko Bala MAB/LMJ
November 11, 2021

Tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu na zamanin mulkin wariyar launin fata F.W.de Klerk ya rasu a gidansa da ke Cape Town yana da shekaru 85. Ya taba samun lambar yabo ta Nobel.

https://p.dw.com/p/42sDY
Frederik Willem de Klerk
Hoto: Herbert Neubauer/picture alliance

De Klerk ya jagoranci Afirka ta kudu a karshen wa'adin mulkin wariya kafin daga bisani marigayi Nelson Mandela ya zama shugaba a 1994. De Klerk ya karbi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel tare da Nelson Mandela wanda suka yi aiki tare wajen kawo karshen wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. Ya rasu sakamakon cutar cancer bayan ya sha fama da jinya. 

Wani mai magana da yawun gidauniyar F.W.De Klerk ya tabbatar da rasuwarsa a wannan Alhamis 11.11.2021). FW De Kler ya yi kaurin suna a Afirka ta Kudu inda mutane da dama suka zarge shi da kuntata wa bakar fata 'yan Afirka ta Kudu da masu fafatukar yaki da wariyar launin fata a zamanin mulkinsa.