1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fusatar Italiya game da mutuwar ɗanta a sokoto

March 9, 2012

Shugaban Italiya ya soki lamirin Birtaniya game da mayar da ƙasarsa saniyar ware lokacin da ta yi yunƙurin kuɓutar da turawan da aka yi garkuwa da su a sokoton Najeriya.

https://p.dw.com/p/14IGt
Italian President Giorgio Napolitano, listens to questions during a joint press briefing with Romanian counterpart Traian Basescu, not in picture, in Bucharest, Romania, Thursday, Sept. 15, 2011 at the Cotroceni Presidential Palace. (AP Photo/Andreea Alexandru/Mediafax Foto) ROMANIA OUT
shugaban Italiya Giorgio NapolitanoHoto: AP

Shugaba Giorgio Napolitano na ƙasar Italiya ya nuna ɓacin ransa game da gaban kanta da Birtaniya ta yi, na ƙaddamar da yunƙurin kuɓutar da turawan nan da aka yi garkuwa da su a Sokoton Najeriya. A lokacin da ya ke amsa tambayoyin manaima labarai bayan fitowarsa daga majalisar dokoki, shugaban na Italiya ya ce wannan mataki da hukumomin London suka ɗauka bai dace ba a hulɗa tsakanin ƙasa da ƙasa ba.

Sai dai kakakin gwamnatin Birtaniya ya bayyana ɗazu ɗazunnan cewar takwarorinsu na Italiya na da masaniya game da yunƙurin ceto turawan da aka yi garkuwa da su tun watan mayun bara. Wani ɗan Italiya na daga cikin turawan biyun da suka rasa rayukansu a birnin na shehu bayan da yunƙurin cetosu ya ci tura.

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewar ita ta shirya wannan yunƙuri tare da haɗin guywar gwamnatin Najeriya. Tun a shekarar da ta gabata ne dai aka yi garkuwa da waɗannan turawan a jihar Kebbi. Waɗanda suka shaidar da misayar wuta tsakanin jami'an tsaro da kuma waɗanda suke tsare da turawan suka ce mutane biyar ne suka ransa rayukansu a ranar ta alhamis.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala