Fursunoni 900 sun tsere a Kwango | Labarai | DW | 11.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fursunoni 900 sun tsere a Kwango

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani gidan yarin arewa maso gabashin kasar, inda suka kashe mutane 11 sun kuma bai wa daruruwan fursunoni damar tsarewa a inda ake tsare da su.

Gwamnan Arewacin Kivu Julien Paluku ya ce maharan da ba'a kai ga tantace inda suka fito ba, sun yi amfani da man'yan makamai a yayin harin inda suka kashe jami'ai tsaron gwamnati takwas da kea gadin yarin. Kawo yanzu dai babu kungiyar da ta dau alhakkin harin.

A ranar Asabar da ta gabata wata kafar sadarwar internet a kasar da ma bayanan daga hukumomin 'yan sanda, sun ruwaito wata kungiyar addini da ke labewa da siyasa, mai suna "Bunda dia Kongo", ta kai wani hari a ofishin mai shigar da karan gwamnati tare da kai wani hari a ofishin 'yan sanda da ke Kinshasha babban birnin kasar. A yanzu dai tuni hukumomin tsaro suka ayyana dokar ta-baci a garin na Beni da aka kai harin.