Frashin man fetir ya faɗi a bisa kasuwannin duniya | Labarai | DW | 27.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Frashin man fetir ya faɗi a bisa kasuwannin duniya

Ministocin samar da makamashi da man fetir na ƙasashe masu arzikin man fetir OPEC sun gaza cimma matsaya guda wajen rage yawan man fetir ɗin da ake haƙowa a kowace rana.

Ministocin na OPEP sun fara yin wani taro a birnin Vienna domin duba mataki da za su ɗauka dangane da faɗuwar frashin man fetir ɗin a bisa kasuwanin duniya.

Amma kuma ba tare da cimma wata matsaya guda ba, a game da yadda za su rage yawan gangar ɗayan man fetir da ake haƙowa a kowace rana. Da yake magana da manema labarai minista mai da kuma samar da Makamashi na Saudiyya, ya ce suna neman daidaita kasuwar man na wani lokaci mai tsawo.