Firsinonin Palasdinu sun samu ′yanci | Labarai | DW | 30.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firsinonin Palasdinu sun samu 'yanci

Akwai yiwuwar Palasdinawa su dan samu saukin danniyar da Yahudawa 'yan kama wuri zauna ke musu.

Gwamnatin kasar Isra'ila ta kammala kashi na biyu daga cikin hudu na sakin firsinoni Palasdinawa da take tsare da su a gidajen yarin kasar, inda da sanyin safiyar yau aka saki Palasdinawan 26 daga gidan yari.

Rahotanni sun bayyana cewa 20 daga cikin firsinonin sun shiga Palasdinu ta kan iyakar kasar da Isra'ila dake gabar yammacin kogin Jordan, yayin da sauran biyar kuma suka tsallaka zuwa Palasdinun takan iyakar kasar da Isra'ila dake yankin Zirin Gaza.

Sakin firsinonin dai na daga cikin matakan sulhu da aka cimma a tattaunawar da aka yi tsakanin kasashen biyu a baya bayan nan, duk kuwa da cewa Yahudawan Isra'ilan 'yan kama wuri zauna na adawa da sakin firsinonin da suka bayyana da 'yan ta'adda.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu