Firimiyan Afrika ta Tsakiya ya yi murabus | Labarai | DW | 05.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firimiyan Afrika ta Tsakiya ya yi murabus

Yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya ce ta tanadi Firaminista Nzapayéké ya sauka domin a samu maslaha a rikicin addini da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke fama da shi.

Firaministan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya André Nzapayéké ya yi murabus domin bai wa kasarsa damar magance rikicin addini da ta shafe watanni tana fama da shi. Yarjejeniyar zaman lafiya da bangarorin da ke fada da juna suka cimma a birnin Brazaville na Kwango ne, ya tanadi rusa gwamnatin da take ci yanzu da nufin kafa sabuwa da za ta samu karbuwa ga kowa da kowa.

Kakakin fadar shugabar kasar ya bayyana cewar gwamnatin da Shugaba Catherine Samba Panza za ta kafa, za ta kunshi kwararru da 'yan siyasa tare kuma da yin la'akari da kabilun da kuma addinan da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta kunsa.

Yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan Seleka da kuma Anti-Balaka suka amince da ita ce, ta sa an samu sararawa a 'yan kawanakin baya-bayan nan a fadace-fadacen da Musulmin da Kiristocin kasar ke yi.

Ita dai gwamnatin da aka kafa watanni bakwan da suka gabata, ta kasa shawo kan rikicin da ya lashe dubban rayuka, tare da jefa tattalin arzikin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya cikin wani mawuyacin hali.

Mawalafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal