Firayim ministan Lebanon ya yi murabus | Labarai | DW | 23.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firayim ministan Lebanon ya yi murabus

Najib Mikati ya ce ya sauka daga muƙamin ne sabo da rashin jituwa da ke tsakaninsa da Hezbollah, abin da ya kawo cikas wajen gudanar da harkokin mulki.

Najib Mikati wanda ke riƙe da wannan matsayin tun a cikin watan Yuni na shekara ta 2011. Ya ce ya ajiye aikin ne saboda saɓannin da ke tsakaninsa da abokan ƙawancensa na Hezbollah, akan maganar zaɓen yan' majalisun dokokin wanda za a gudanar a cikin watan Yuni da ke tafe.

Da kuma kan batun ƙara tsawaita wa'adin aikin shugaban rundunonin tsaro na ƙasar, Janar Achraf Rifi wanda wa'adin aikinsa ke kammala a ƙarshen wannan wata. Jam'iyyun siyasar dai masu ra'ayin Kristanci na buƙatar da a sauya kudin zaɓe na ƙasar wanda a ka kirkiro tun a shekara ta 1960, wanda suka ce ya na ba da fifiko ga musulumi mafi rinjaye. Ya kuma ce ya sauka ne daga muƙamin domin ba da wata dama ta a tattauna domin warware cikas ɗin da a ke samu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman